
Kamfanonin Dangote ne suka zo na daya a Nahiyar Africa wajan samar da kayan Masarufi na yau da kullun a shekarar 2025.
Kafar The African Exponent ce wadda ta shahara wajan samar da bayanan kasuwanci ta bayyana hakan.
Face Dangote ya zo na daya da kamfanoninsa na Sugar, Gishiri, Taliya da Macaroni da sauransu.
Kamfanin Nestlé dake yin Milo, Nescafé, Cerelac, da Maggi ne ya zo na biyu inda yake da rassa a kasashen Nigeria, Ghana, South Africa, da Côte d’Ivoire.
Daga nan kuma sai kamfanin Unilever wanda ya zo na 3, shine ke yin OMO, Close-Up, Lipton, Vaseline, da magin Knorr.
Kuma yana da rassa a kasashe kusa 20 na Afrika.
Kamfanin Africa ta kudu me sunan Tiger Brands ne ya zo na 4.
Sai kamfanin SABMiller AB InBev wanda shima na kasar Africa ta kudi ne ya zo na 5.
Kamfanin Société Anonyme des Brasseries du na kasar Kamaru ne na zo na 6.
Sai kamfanin Fan Milk yazo na 7.
Kamfanin Dufil Prima Foods ne ya zo na 8.
Rahoton yace ana samun ci gaba wajan masana’antun kayan masarufi a Africa.