A yayin da ranar auren taurarin fina-finan Hausa, Abdul M. Shareef da amaryarsa, Maryam Malika ke kara matsowa, Masana’antar Kannywood sai nuna doki take.
Da farko dai ganin katin gayyatar auren ne ya fara daukar hankulan mutane inda aka ga cewa ranar 27 ga watan Yuni ne za’a daura auren.
Bayan nan kuma sai Hotunan kamin boki ke ta fitowa daga manyan jaruman masana’antar.
Ali Nuhu na daga wadanda suka watsa hotunan bikin:

MC Ibrahim Sharukhan ma ya wallafa hotunan bikin inda yake ma sabbin ma’auratan fatan Alheri:

Shima Alhaji Shehe ya wallafa hotunan auren:

Muna fatan Allah ya sanya Alheri ya kaimu Lafiya.