
Tun bayan rasuwar Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi ƴan Najeriya musamman Musulmai ke ta faman yi masa addu’o’on nema masa gafara da kuma yin tambayoyin sanin haƙiƙanin wane ne marigayin.
Hakan ne ya sa BBC ta ji ta bakin Injiniya Ayuba Abdullahi Muhammad wanda ɗalibinsa ne kuma makusancinsa.
Haihuwa
An haifi Malam Idris Abdu’aziz Dutsen Tanshi a garin Gwaram da ke ƙaramar hukumar Alƙaleri a jihar ta Bauchi a shekarar 1957.
Marigayin ya yi doguwar jinya kafin rasuwar tasa, inda ya yi yawon neman magani a ƙasashen da suka haɗa da Saudiyya da Indiya.
Sheikh Tanshi ya rasu ya bar mahaifiyarsa da mata guda uku da kuma ƴaƴa 32.
Ilimi
Sheikh Idris Abdul’aziz ya kasance mutum mai son neman ilimi musamman bincike. Ya ƙware a fannin Shari’ar Musulunci inda ya yi digirinsa na ɗaya da na biyu da na uku duka a fannin na Shari’a.
Ya halarci jami’ar Madina da Sudan da ta Jos da BUK da ke Kano sannan kuma ya yi wasu kwasa-kwasai.
“Daga fitowar Alfijir har zuwa faɗuwar rana babu abin da Malam yake yi idan ba harkokin ilimi ba walau dai bayar da ilimin ko kuma yin bincike.” In ji Injiniya Abdullahi Muhammad.
Faɗin gaskiya
Injiniya Abdullahi ya ce mutane ba su san haƙiƙanin “halin malam ba. Shi mutum ne mai tsananin son faɗin gaskiya kuma ba ya ɓoye-ɓoye. A duk lokacin da ya karanta wani ilimi kuma ya fahimci al’amari to zai fito ya faɗ shi ba tare da nuƙu-nuƙu ba.
Dangane kuma da yadda jama’a ke kallon malamin a soshiyal midiya, Injiniya Abdullahi ya ce “duk wannan hargagin da jama’a ke gani a sohiyal midiya ba haka malam yake ba. Idan ka ga malam ya yi wa mutum faɗa to ka tabbata sai bayan ya nanata yi maka magana sau biyu ko uku.
Sannan kuma akwai wani abu, idan malam ya yi maka magana ko kuma samu saɓani ta fahimta to ka tabbatar da zarar ya faɗi ra’ayinsa to wallahi wannan ya wuce. Ba ya riƙe mutane a ransa.” In ji makusancin nasa.
Ya ƙara da cewa “malam mutum ne mai sauƙin kai amma sai ka matso kusa da shi za ka gane. Mutum ne mai son jama’a da son taimaka musu da kuma yi musu gargaɗi.”
Sana’a
Injiniya Ayuba ya ce saɓanin malamai mafi yawa da suka mayar da malanta sana’a, shi marigayi Sheikh Dutsen Tanshi ɗn kasuwa ne.
“Yana noma sosai domin daga safe har lokacin da zai bayar da karatu malam yana gona. Sannan yana da makarantun nazare da firamare da kwalejin ilimi a Bauchi.
Yana kuma da shagunan kayan masarufi da na kayan sha da kuma irin waɗanda ake kira ‘business centres da na magunguna.” In ji Injiniya Ayuba.
Zumunci da ayyukan jinƙai
“Malam yana ɗaukar mota ya cika ta da ƴaƴansa su tafi ƙauyensu domin sada zumunci da ƴanuwansa. Kuma idan ya tashi zuwa zai tafi da kuɗi ne yi musu kyauta. Malam mutum ne mai zumunci. Yana ƙaunar ƴanuwansa sannan yana taimaka musu.” In ji Injinya Ayuba.
Dangane kuma da ayyukan jinƙai na marigayin ke yi, makusancin nasa ya ce ” idan ka shiga azuuwan makarantar malam za ka adadi mai yawa na marayu da suke yin karatu kyauta sannan kuma yana saya musu littafai na sauran kayan karatu.
“Akwai ma wani lokacin da a ka shiga yanayin tsanani a ƙasar kamar shekaru biyu baya, da malam ya lura da hakan sai ya ce malam ya lura da yanayin tsananin da ake ciki jama’a na fama da kuɗin abinci ba ta karatu suke yi ba, sai malam ya ce ya yafe wa kowa kuɗin makaranta. Kowa zai yi karatu kyauta a lokacin.” In ji Injiniya Ayuba Abdullahi makusancin marigayi Sheikh Idris Abdul’aziz.
Yadda aka yi jana’izar Sheikh Idris Dutsen Tanshi
An yi jana’izar fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na jihar Bauchi, Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi, da misalin ƙarfe 10 na safiyar yau Juma’a a birnin Bauchi.
Dandazon al’umma ne suka halarci taron jana’izar tasa da aka gudanar a masallacin Idin malamin na Games Village, da ke birnin Bauchi.
Sheikh Dutsen Tashi dai ya rasu da misalin karfe 11 na dare ranar Alhamis, a gidansa da ke Bauchi, bayan fama da jinya.
Kungiyar Jama’atul Izalatul Bidi’a Wa’iqamatus Sunna JIBWIS da sauran manyan malamai tuni suka fara aikewa da sakon ta’aziyya tare da alhinin mutuwar malamin.