
Tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Ifeanyi Okowa wanda ya koma APC yace ba’ masa Adalci ba labarin da aka rika yadawa wai yace yayi dana sanin yiwa Atiku takarar mataimakin shugaban kasa a zaben 2023.
Okowa yace shi bai fadi haka ba, yace abinda ya fada a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV shine, ya lura mutanensa basa son zaben dan Arewa, dan kudu suke son zaba.
Yace amma duk da haka bai ki ci gaba da takara da Atiku ba.
Okowa ya bayyana hakanne ta bakin tsohon kakakinsa wanda a yanzu shine kakakin gwamnan jihar Delta, Mr Olisa Ifeajika inda yace ‘yan jaridar da suka wallafa wancan labarin basu wa Okowa Adalci ba.