
Basaraken Yashirika na karamar hukumar Baruten jihar Kwara ya bayyana cewa maganar bullar ‘yan Bindiga a karkashin masarautarsa gaskiyane.
Yace amma abin takaici shine yanda jami’an tsaro ke karyata ikirarin nasu.
Yace sun sayo motar da ‘yan banga ke amfani da ita suna samar da tsaro a yankin nasu amma wadannan sabbin ‘yan Bindiga masu suna Mamuda sun lalata motar.
Yace kuma maganar kisan da ‘yan Bindigar sukawa mutanensu gaskiya ne amma bai kai 15 ba da ake cewa inda yace kuma kowane bangare ya fuskanci asara.
Saidai hukumar ‘yansandan jihar ta bakin kakakinta, SP Adetoun Ejire-Adeyemi tace maganar kisan mutane 15 da aka ce an yi karyane.
Sannan yace sun bincika basu gano wata sabuwar kungiyar ‘yan ta’adda me suna Mamuda ba.
Yace suna baiwa mutane tabbacin samar da tsaro a jihar.