Friday, December 5
Shadow

Karya ministan Lafiya yake, bamu janye yajin aiki ba>>Inji Kungiyar malaman Jinya(Nurse) na Najeriya

Kungiyar malaman jinya(Nurse) da Ungozoma (NANNM-FHI) sun bayyana cewa, basu janye yajin aikin da suka shiga ba na kwanaki 7.

Kungiyar ta nesanta kanta da kalaman Ministan lafiya, Prof. Muhammad Pate wanda a dazu bayan kammala zaman tattaunawa dasu yace sun amince su janye yajin aikin.

Me magana da yawun kungiyar, Omomo Tibiebi ne ya bayyana haka inda yacw yajin aikin da suka fara tun ranar Laraba har yanzu basu janye ba.

Yace ba ministan ne ya ke yajin aikin ba, dan haka bashi da hurumin janye yajin aikin.

Yace sai a ranar Asabar ne zasu zauna dan tattauna batun da duba irin alkawarin da gwamnatin ta musu ko abune da zasu iya amincewa dashi ko kuwa a’a.

Karanta Wannan  Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya fara yakin neman zaben 2028 inda yake neman zama shugaban kasa a karo na 3 duk da kundin tsarin mulkin kasar Amurka ya hana hakan

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *