
Rahotanni daga kasar Angola na cewa kasar ta karrama tsohon shugaba Mulkin soja na Najeriya, Janar Murtala Ramat Muhammad saboda taimakon da ya bayar wajan ci gaban Nahiyar Afrika
Hakanan cikin wadanda aka karamma akwai tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo da Farfesa Ibrahim Gambari.
An yi bikin karramawar ne a babban birnin kasar me suna Luanda.