
Kasar Iran ta kàshè wani dan kasarta me suna Pedram Madani dan kimanin shekaru 41 wanda ijiniya ne saboda samunsa da laifin yiwa kasar Israyla leken Asiri a Iran din.
An kashe shine ta hanyar Rataya bayan samunsa da laifin haduwa da wakilan kungiyar leken Asirin kasar Israela ta Mossad da karbar kudi yana musu aiki.
An ratayeshine ranar 28 ga watan Mayu a gidan yarin Ghezelhesar Prison, Karaj.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sun yi Allah wadai da lamarin.