Kasar Iran ta samar da gidan mahaukata a babban birnin kasar, Tehran inda za’a rika kai mata dake kin saka Hibaji dan kula dasu.
An dai sakawa asibitin sunan Clinic for Quitting Hijab Removal, tun a shekarar 2022 ne dai kasar ke fama da masu fafutuka dan ganin an daina tursasa sanya Hijabi a kasar.
Jami’ar da zata rika kula da wannan asibiti me suna Mehri Talebi Darestani tace an budeshine musamman saboda koyawa yara mata kyan al’adarsu da kuma muhimmancin hakan a addinin Musulunci.