Wednesday, March 19
Shadow

Kaso 90 cikin 100 na Kiristocin da ake ķķàshèwà a Duniya a Najeriya ake ķķàshèsu, Najeriya ta kasa baiwa Kiristoci kariya dan haka zamu Kakaba mata Takunkumi>>Inji Kasar Amurka

Majalisar kasar Amurka ta baiwa shugaban kasar, Donald Trump shawarar ya kakabawa Najeriya takunkumi saboda yawan kashe kiristoci da ake yi a kasar.

Majalisar ta cimma wannan matsayane bayan samun bayanai daga wani bincike da aka gudanar da yake nuna cewa kaso 90 na kiristocin da ake kashewa a Duniya a Najeriya ne hakan ke faruwa.

Majalisar ta kasar Amurka ta zargi Najeriya da kasa daukar matakan da suka kamata dan baiwa Kiristocin kariya daga hare-haren ta’addanci dake yin sanadiyyar mutuwarsu.

Saidai a martanin Gwamnatin Najeriya tace wannan magana ba gaskiya bace.

Sanarwar da ma’aikatar harkokin kasashen waje ta Najeriya ta fitar ta hannun kakakinta, Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya bayyana cewa, tabbas akwai matsalar tsaro a Najeriya.

Karanta Wannan  Bankin First Bank ya kori ma'aikata 100

Amma ba wani addini daya aka ware shi kadai ake kai masa hari ba, harin yana shafar kowa da kowane ko kuma ace kan mai uwa da wabi.

Ma’aikatar ta bayyana cewa, gwamnati na daukar matakin magance matsalar tsaro na karfi da bana karfi ba.

Inda ta bayar da misalan nasarorin da sojojin Najeriya suka samu da kuma sulhu da ake yi da ‘yan Bindigar a wasu lokuta da kuma samar da ma’aikatar kiwo.

Ma’aikatar ta harkokin kasashen waje ta jawo hankalin kasashen Duniya da su rika tantance ingancin labari kamin su dauki mataki akansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *