
Rahotanni sun ce kasuwar Kirypto ta tafka gagarumar Asarar da ba’a taba ganin irinta ba a Tarihi.
Rahotanni sun ce a cikin awanni 24, kasuwar ta tafka asarar dalar Amurka Biliyan $19.6.
Hakan na zuwa ne bayan da shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya sanar da shirin kakabawa kasar China sabon haraji na kaso 100.
Hakanan labarin cewa an yiwa manhajar Binance kutse ya kawo tarnaki a kasuwar ta Crypto inda daga baya mutane suka kasa amfani da Binance din da Coinbase.
Saidai an ga wani sun kintaci wannan yanayi sun ci ribar makudan kudade wanda hakan yasa ake zargin cewa ko dai da gangan aka yi hakan ko kuma sun samu bayanan sirri game da karyewar kasuwar.