
Mutanen Arewa ta tsakiya da suka hada da Kiristoci da Maguzawa, da mutanen jihar Jos da sauransu sun bayyana cewa, basa tare da sauran mutanen Arewa dake cewa basa son Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Sun bayyana cewa su a shekarar 2027, Shugaba Bola Ahmad Tinubu ne zabinsu.
Saidai wadannan mutane dake son ballewa dan nuna goyon bayan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, kalilan ne daga cikin mutanen Arewa.
Saidai a gefe daya kuma, Mafi yawan ‘yan Arewa sun bayyana cewa basa tare da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu inda suka ce ba zasu zabeshi ba a zaben 2027.
Kungiyoyin fafutuka da yawa daga Arewa sun bayyana cewa ba zasu goyi bayan sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a shekarar 2027 ba.
Shugaban kungiyar hadaka ta kungiyoyin Arewar, Jamilu Charanchi ya bayyana cewa matukar wahalar rayuwa da matsin tattalin arziki ya ci gaba a Najeriya, ‘yan Arewa ba zasu zabi Bola Ahmad Tinubu a shekarar 2027 ba.