
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya bayyana cewa, a shekarar 2027 ‘yan Najeriya APC zasu zaba daga sama har kasa.
Ya bayyana hakanne a ranar Asabar a Dandalin Murtala dake Kaduna inda aka yi bikin karbar wasu sabbin ‘yan jam’iyyar APC.
Yace ‘yan Najeriya zasu sabi APC dinne saboda Adalcin data musu.
Ya kara da cewa a shekarar 2027 za’a sake zabar Tinubu a matsayin shugaban kasa inda kuma za’a sake zabarsa a matsayin gwamna sannan duka ‘yan majalisar wakilai da jihohi ma haka.
Yace sabbin ‘yan jam’iyyar da suka shigo ba za’a nuna musu wariya ba, zasu samu iko kamar kowane dan Jam’iyyar inda yace kan Jam’iyyar APC a hade yake.