
Tsohon Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya bayyana cewa kudancin Najeriya gaba daya na Shugaba Tinubu ne.
Yace Tinubu kuri’u kadan yake bukata daga Arewa ya ci zabe.
Fayose ya bayyana hakanne a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.
Yace Peter Obi ne zai zo na 2 sannan sai jam’iyyar ADC zata zo na 3 sai watakila PDP ta zo na 4.
Ya bayyana cewa idan aka lura da Tarihin da Tinubu ya kafa a siyasar Najeriya, da wuya ya fadi zaben 2027.