
Tsohon gwannan jihar Bayelsa, Sanata Seriake Dickson ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa, Marigayi Muhammadu Buhari na da gaskiya inda yace babu wanda ya kaishi gaskiya a cikin ‘yan siyasar Najeriya.
Ya bayyana hakane a zauren majalisar Dattijai inda yace Buhari na da karamci da kima sosai.
Ya bayar da labarin yanda Kotu ta tsige gwamnan APC a jihar Bayelsa kuma shugaba Buhari ya yadda da hukuncin ba tare da ja ba.