
Fadar shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, bata kadu da barazanar kawo Khari ta kasar Amurka zuwa Najeriya ba.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai bayan zaman majalisar zartaswa.
Yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu bai kadu ba, hakanan Ministocinsa basu kadu ba da barazanar kasar Amirka ta kawo hari ba.
Yace saidai tuni suka nema suka fara tattaunawa da wakilan kasar Amurka, yace suna bin hanyar Diplomaciyya dan warware matsalar.