Babbar Kotun tarayya dake Abuja inda aka gurfanar da yaran da gwamnati ke zargi da cin amanar kasa ta bayar da umarnin a kaisu gidan yari a ci gaba da tsaresu har sai ranar 1 ga watan Janairun 2025 sannan a ci gaba da shari’a.
Saidai a wani sabin rahoto da hutudole ya samu, babban lauyan Gwamnati ya bukaci a mayar da maganar shari’ar yaran ofishinsa inda kuma ya nemi a dawo da ranar ci gaba da shari’ar kusa.
A wata majiya daga ma’aikatar shari’ar tace ana tsammanin nan da ranar Talata me zuwa za’a iya dawowa a ci gaba da shari’ar sannan kuma gwamnati na shirin janye zargin da takewa yaran.