Friday, December 5
Shadow

Kotu na da hurumin sauraron ƙara kan masarautar Kano

Wata babbar kotu a Kano ta yanke hukuncin cewa tana da hurumin sauraron ƙarar da aka shigar kan rikicin masarautar Kano, musamman kan abin da ya shafi kare hakkin ɗan’adam bisa dogaro da sashe na 46 na kundin tsarin mulkin Najeriya.

Alƙalin kotun, mai shari’a Liman Mohammed na babbar kotun tarayya da ke jihar, ya yanke hukuncin cewa tsohon sarki Aminu Ado Bayero na da damar a saurare shi a kotu.

Sai dai alkalin ya ce ba magana ce a kan cancantar majalisar dokokin jihar na sauya dokar masarautun jihar ko kuma a’a ba.

Alƙalin ya bayyana cewa kotun ba ta ƙalubalantar damar da gwamnatin jihar ke da shi na naɗawa ko sauke sarki.

Karanta Wannan  An kama Alkali da zargin satar kudi a asusun me laifi da aka kai kotu ake tuhumarsa a Kano

A ranar 23 ga watan Mayu ne gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun Kano ta 2024, bayan majalisa ta amince da ita.

Wannan ne ya bayar da damar komawar sarkin Kano na Muhammdu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16 tare da cire Aminu Ado Bayero daga kan mulki.

Sai dai jin kaɗan bayan haka ne Aminu Babba Danagundi ya shigar da ƙara yana ƙalubalantar sabuwar dokar, inda kotu ta bayar da umurnin tsayawa kan matsayin da ake.

Sai dai lamarin ya janyo ruɗani, inda Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II kowannensu ke iƙirarin shi ne halastaccen sarki.

Karanta Wannan  Kowane Musulmi Imaninsa Yana Cika Ne Idan Ya Yarda Tare Da Rungumar Kowace Irin Kaddara Ce Ta Same Shi, Cewar Sarki Sanusi II A Hudubarsa Ta Yau Juma'a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *