
Babbar kotun tarayya dake Maitama Abuja ta sanar da bayar da Belin Tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele akan Naira Biliyan 2.
Ranar Litinin ne kotun ta bayar da belin Emefiele bayan da aka gurfanar dashi bisa zarge-zargen cin hanci da rashawa guda 8 ciki hadda gina rukunin gidaje 753 a Abuja.
An kuma zargeshi da amfani da wasu mutane ‘yan uwa da abokai wajan satar kudaden Gwamnati.