
Fitattaccen lauya mai rajin kare haƙƙin ɗan’adam a Najeriya, Barista Hamza Nuhu Ɗantani, ya ja hankalin al’umma da su daina kallo ko ɗaukan abubuwan da ƴan siyasa ko shugabanni suke musu a matsayin taimako ko wata alfarma domin ba da kuɗinsu suke yin ayyukan ba.
Barista Ɗantani wanda ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito, ya fara ne da cewa, “Ba fa noma ko wani aiki suka yi aka biya su suke muku aiki da kuɗin ba! Ba Kuɗinsu ba ne! Ba Dukiyarsu Ba ce! Ba Guminsu ba ne! Su da kansu suka fito suka roƙe ku don ku zaɓe su! Suka dinga manna hotunansu (Posters), suna ta ihu suna shiga lungu da saƙo suna barar ƙuri’unku don kawai su riƙe amanar Dukiyarku!”. Inji shi.
Barista Ɗantani, ya ci gaba da cewa, “Ku sani Haƙƙinku ne, ba fa kuɗinsu ba ne, ba dukiyarsu ba ce! Su ne suke cin alfarmarku, suke shiga rigar dukiyarku suna kuma watayawa da dukiyarku.
Ya kamata mutane su sani cewa Shuwagabanni kamar Su Gwamna a Jiha (Governor of a State) yana nan Kamar mai riƙon amana ne ! Dukiyar talakawan Jiharsa ake ba shi ya riƙe musu amana. Don Gudanar da kykkyawar gwamnati tare da walwala da jin daɗin mutanensa!
Kuma haƙƙi ya rataya a kan kowane ɗan Jiha ya bibiyi yadda aka kashe wannan dukiyar. Sashi na 1 na dokar bayar da bayanai, (Freedom of Information Act 2011), ya ba wa kowane ɗan ƙasa damar bibiyar cikakken bayanin kashe dukiya ko neman wani bayani akan aikace-aikacen gwamnati.
Sashin yane cewa: ”Kowane mutum yana da haƙƙin samun damar ko neman kowane irin bayani wanda ke wajen kowane jami’in gwamnati, hukuma ko wata cibiya da aka kafa”.
Ku sani cewa, gwamnatin tarayya, (Federal Goverment) ke da alhakin turawa kowace Jiha kuɗinta, (Grant Allocations) don su biya ma’aikatan gwamnati da kuma yi wa Jiha Aiki. Duk da ma cewa ita kanta Jihar tana samun wasu kuɗaɗen shiga masu yawan gaske ta fannoni da dama a cikin Jiharta, ban da wasu taimakon kuɗaɗe da wasu ƙasashen waje ke bayarwa!
Ku sani cewa, amana ce fa! Don ka fita ka tofa albarkacin bakinka ko kuma ka ƙalubalanci yadda gwamnati take tafiyar da al’amarinta, ba laifi ba ne kuma ba cin mutunci ko zagi ba ne.
Ina mamakin mutumin da za a zaɓe ka, ka yi wa mutane alƙawarori da dama, ka saka wa mutane tsammanin gyara da riƙon amana amma daga mutum ya ƙalubalence ka, sai ka sa a kama shi, akulle shi! Ko kuma ka ce kai ba ka son a yi maka zaɲģa-zaɲģã (Protest!).
Kuma fa, zanga-zangar nan, (Protest) ƴanci ne mai zaman kansa wanda yana ƙunshe a sashe na tara (Chapter 9), sakin layi na sha ɗaya, (Article 11, African Charter on Human and Peoples’ Rights) da kuma sashi na 40 na kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yi wa kwaskwarima, (Constitution 1999 as Amended!).
Haka zalika, faɗin albarkacin baki ko ra’ayi shi ma ƴanci ne mai zaman kansa! Yana ƙunshe a sashi na 39 na kundin tsarin mulkin ƙasa (Constitution 1999 as amended)”, cewar Barista Hamza Nuhu Ɗantani.