Wednesday, January 15
Shadow

Ku daina Tsinuwa da zagi ga shuwagabanni, Addu’a ya kamata ku rika musu>>Sarkin Musulmi ga ‘yan Najeriya

Me Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na II ya yi kira ga ‘yan Najeriya su daina tsinewa da kuma la’antar shuwagabanni inda yace su mayar da komai ga Allah.

Yace ‘yan kasa su rika yiwa shuwagabanni addu’a da ma kasar baki daya.

Yace babu wani abu me kyau ko marar kyau dake dawwama,koma menene zai wuce kamar ba’a yi ba.

Ya kuma jawo hankalin shuwagabanni dasu san cewa zasu tsaya a gaban Allah dan amsa yanda suka gudanar da mulki inda babu wanda zai karesu.

Sannan yayi kira ga malamai da su rika gayawa mabiyansu gaskiya.

Sarkin yayi wannan jawabine a wajan wani taro da ya gudana a Kaduna ranar Litinin inda aka hada malaman Addinin Musulunci da Kiristanci.

Karanta Wannan  JARABTA: Cikin Kwanaki Uku A Jere, Ya Rasa Matarsa Da Yaransa Biyu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *