Friday, June 26
Shadow

Ku Daina Watsa labaran mutanen Daji: Gwamnatin tarayya ta gargadi gidajen Jaridu

Gwamnatin tarayya ta gargadi gidajen Jaridu da cewa, su daina yada labaran tsageran daji.

Hakan ya fito ne daga bakin ministan yada labarai Muhammad Idris a wajan wani taro da aka shirya da hadin gwiwar hukumar DSS da kafafen watsa labarai.

Yace abin yana bashi takaici yaga shafukan farko na jaridun Najeriya na magana akan harkokin mutanen Daji yayin da ba’a son watsa nasarorin sojoji.

Yace wannan abu na watsa labarin abinda tsageran daji suke yi su dama abinda suke son a yi kenan gashi kuma ana musu shi kyauta.

Yace ya kama masu kawo rahoto da masu tacewa su san labarin da ya kamata a yada da wanda bai kamata a yada ba dan tsaro da ci gaban kasa.

Karanta Wannan  BA RABO DA GWANI BA: Yau Shekara 15 Da Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa Ummaru Musa Yar'adua

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *