Friday, October 2
Shadow

Cire Naira Biliyan 500 da gwamnatin tarayya ta yi daga Asusun Hadakar Gwamnatoci ya dauki hankula

Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta cire naira Biliyan 500 daga asusun hadakar Gwamnatoci kamin a raba kudaden shigar da aka tare tsakanin Gwamnatocin Tarayya, Jihohi da Kananan Hukumomi.

Wata Majiya ta tabbatarwa da Jaridar Punchng cewa lallai an cire kudin wanda aka ware dan ko ta kwana musamman a bangaren tsaro.

Jaridar tace akawun jihohi wanda dasu ake aikin raba wadannan kudade basu yi korafi akan cire wadannan kudade ba wanda hakan ke nuna cewa suna sane da hakan.

A baya ma dai an cire jimullar Naira Biliyan N952bn inda aka baiwa Sojoji, da wasu ma’aikatun Gwamnati da yin ayyukan ci gaba a wasu jihohi.

Karanta Wannan  Allah Sarki: Kalli bidiyon Yanda wannan malamin ya sassauta lafazi akan Rasuwar Habu Dan Damisa, Yace Lamarinshi na gurin Allah a daina munana masa zato, bayan da a baya yayi wa'azi me kaushi sosai akan Dan Damusa amma yaran Dan Damusa suka gargadeshi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *