
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya baiwa matasan Najeriya shawarar su daina zaben shugaban kasa bisa banbancin Addini ko Kanilanci.
Yace su rika zabe saboda cancanta.
Jonathan yace banbancin Addini da Kabilanci na daga cikin abinda ke hana kasarnan ci gaba.
Jonathan yace abin na damunsa kuma idan ba’a gyara ba, haka za’a ci gaba da tafiya har ‘ya’ya da jikoki.
Yace mafi yawancin matsalolin da muke fuskanta a kasarnan duk saboda wannan matsala ce ta nuna banbancin Addini da kabilanci.
Jonathan yace a irin wannan tsari da wuya a samu shugaba na gari.