Gwamnatin Tarayya ta baiwa ‘yan Najeriya shawarar cewa su daina kashe kudi barkatai.
Tace su rika lissafi da iyalansu suna kiyaye yawan kudaden da zasu kashe.
Ministan kasafin kudi da tsare-tsare, Atiku Bagudu ne ya bayyana haka.
Ministan yace Najeriya bata da kudin da ake tsammani dan haka kasar da mutanen kasar su san irin yawan kudin da zasu rika kashewa.
Yayi bayanin ne a Abuja a wajan watan ganawa tsakanin Gwamnatin tarayya da wakilan kungiyar kwadago na NLC da TUC.
Hakan na zuwane a yayin da ake fama da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa a Najeriya.
Minista Bagudu ya goyi bayan tsare-tsaren Gwamnatin tarayyar inda yace sun samu kudi kuma zasu gudanar da tsari me kyau a kasarnan.