
Kafafen sada zumunta sun karade da wasu kalamai da ake zargin Ministan Abuja, Nyesome Wike da furtawa akan Arewa.
Kalaman dai sun baiwa mutane mamaki matuka ace daga bakin Wike suka fito saidai sanin yanda yake da katobara, wasu sun ce basu yi mamakin jin cewa ya fadi hakan ba.
Rahotannin dai na cewa, Wike yace ne a kyale ‘yan Arewa surutu kawai suke, nan da shekarar 2027 yunwar da zata kama su da kansu zasu rika rokon a basu dubu biyu su zabi APC.
Zuwa Yanzu dai Wike be fito ya tabbatar ko karyata wannan kalamai da aka zargeshi da furtawa ba.