Hukumar shige da fici ta kasa ta kama dan daudu, Bobrisky a yayin da yake shirin barin Najeriya.
An kamashine a filin jirgin sama a yayin da yake shirin hawa jirgin sama na KLM zuwa Amsterdam.
Ya bayyana cewa an ji masa ciwo yayin kamen sannan ya zargi cewa hukumar EFCC ce ke da hannu wajan kamun nasa.
Hakanan an ga Bidiyon yanda aka janyoshi daga kan jirgin da karfin tsiya zuwa waje inda da yawa ke tambayar yaya aka yi ya wuce jami’an tsaro ba tare da ganeshi ba.
Wasu dai sun soki yanda aka kamashi inda suke tambayar laifin me ya aikata inda wasu ke cewa an yi daidai kamun da aka masa.