
Rahotanni sun bayyana cewa akwai karin sojoji da zasu bar aiki a Najeriya bayan da shugaba Tinubu ya sauke shuwagabannin tsaron a jiya.
Rahoton wanda Daily Trust ta kawo yace manyan sojoji dake sama da sabbin sojojin da aka baiwa mukaman shugabancin gidan sojan dole su ajiye aiki.
Rahoton yace dama haka tsarin aikin gidan sojan yake dan a ci gaba da samun da’a da yiwa na gaba biyayya.
Hakan na zuwane sati daya bayan da rahotanni suka ce an yi yunkurin yiwa shugaba Tinubu juyin mulki.