Farashin daukar mai a Depot ya karu a ranar Litinin.
Masu Depot dake bayar da sarin man sun kara farashin gangar man da Naira 43 ko ace kaso 4.74 cikin 100, hakan ya farune saboda tashin farashin danyen man fetur.
Wannan na nufin gidajen man fetur da yawa a fadin Najeriya zasu iya kara farashin man da suke sayarwa suma.
Yawancin Depots din sun kafa farashin man da suke sayarwa ne zuwa Naira 950 akan kowace lita kamar yanda jaridar Punchng ta ruwaito.