Tuesday, May 19
Shadow

Najeriya ce kasa ta daya a Afrika sannan ta 2 a Duniya wajan yawan yaran da basu samun abinci me gina jiki>>Inji UNICEF

Najeriya ce kasa ta daya a Afrika sannan ta Biyu a Duniya wajan yawan yaran da basa samun Abinci me gina jiki kamar yanda hukumar kula da yara ta majalisar Dinkin Duniya, UNICEF ta bayyana.

Wakiliyar UNICEF, Nemat Hajeebhoy ce ta bayyana hakan a wajan shirin magance matsalar rashin abinci me gina jiki da ake shiryawa yaran jihohin Adamawa, Borno, da Yobe.

Tace akwai yara guda 600,000 dake fama da matsalar rashin abinci me gina jiki kuma kusan rabinsu na fuskantar kara tsanantar matsalar.

Tace yaran dake fama da matsalar matsananciyar rashin abinci me gina jiki zasu iya mutuwa.

Karanta Wannan  Idan ba'a mana Adalci ba, Toh Wallahi mun san yanda zamu yi mu kutsa cikin garin Uromi a jihar Edo mu dauki fansar 'yan Uwanmu da Akawa Kìsàn Gìllà>>Inji Dangin Mafarautan da aka Kàshè a jihar Edo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *