
Jam’iyyar APC ta yi kira ga shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da ya saka dokar Ta baci a jihar Osun kamar yanda ya saka a jihar Rivers.
Sakataren jam’iyyar APC, Ajibola Basiru ne ya bayyana haka ga manema labarai inda yace a jihar Osun an samu dakile ayyukan kananan hukumomi.
A jiya ne dai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya sanya dokar ta baci a jihar Rivers inda ya dakatar da Gwamnan jihar, Simi Fubara da mataimakinsa da majalisar jihar.