
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya saka dokar ta baci a jihar Rivers.
Ya bayyana hakane a bayanin da yayi da yammacin yau na Talata inda ya sanar da dakatar da Gwamna Simi Fubara.
Hakanan kuma Shugaban kasar ya sanar da dakatar da mataimakin gwamnan na jihar Rivers, Ngozi Odu da duka ‘yan majalisun jihar.
Dakatarwar an yi ta ne na tsawon watanni 6.
An dai samu fasa bututun man fetur a jihar ta Rivers har kusan aau biyu inda shugaba Tinubu yace babu shugaba me hankali da zai ci gaba da kallon wannan abu na faruwa.
Shugaban yace ya baiwa sojoji Umarnin su tabbatar an samu tsaron dukiya da lafiyar jama’a a jihar