
A yayin da ake tsaka da zargin da Sanata Natasha Akpoti kewa kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio na cewa yana son lalata da ita, An gano cewa ta tabata zargin tsohon hadimin shugaban kasa, Reno Omokri da irin wannan zargi.
Saidai duk ba’a gama da wannan ba, har ila yau, Wani bidiyon Sanata Natasha Akpoti ya bayyana inda aka jita tana kuma zargin wani minista da neman yin lalata da ita.
Saidai a wannan karin bata fadi sunan Ministan ba.