
Kungiyar ma’aikatan gidajen mai sun yi Allah wadai da sabunta gidajen man A A Rano ke shirin yi inda yake son kawo tsari irin nankasashen Turai wanda babu me matsa mai saidai me abin hawa ne da kansa zai rika zuba man da kansa.
Sannan gidajen man zasu rika aiki tsawon awanni 24, ma’ana duk tsakar dare mutum zai iya zuwa ya tarar da man fetur ya sha.
Kungiyar ta ma’aikatan gidan man tace idan aka tabbatar da wannan tsarin, zai sa membobinta su rasa ayyukan yi.