Friday, December 5
Shadow

Kungiyar Malaman Jami’a, ASUU ta janye yajin aikin data shiga

Ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU ta dakatar da yajin aikin gargadi na tsawon makonni biyu da ta fara, inda ta bai wa gwamnatin ƙasar wata ɗaya domin ta magance buƙatunta.

Shugaban ƙungiyar, farfesa Chris Piwunayayin wata ganawa da manema labarai, ya ce ƙungiyar ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne domin bai wa gwamnati dama ta nuna kyakkyawan niyya wajen tattauna matsalolin da suka shafi albashi da kayan aiki da inganta yanayin aiki a jami’o’in kasar.

Ƙungiyar ta ce abun da yasa suka janye yajin aikin shine gwamnati ta gabatar da matsayarta kan sabunta yarjejeniysar shekarar 2009 kuma da kiraye-kirayen da suka samu daga mutane da dama daga ƙasar domin sun janye yajin aikin.

Karanta Wannan  Da Duminsa:Hukumar 'yansandan Najeriya ta janyewa Manyan mutanen Najeriya, Irin su Atiku Abubakar, Aisha Buhari, Namadi Sambo da sauransu jami'an 'yansandan dake basu kariya

Wannan ne ya sa ƙungiyar ta bai wa gwamnatin ƙasar wata ɗaya domin ta magance buƙatunta.

Kungiyar ta kuma gargadi gwamnati da kada ta yi wasa da wannan lokaci, inda ta ce idan buƙatun nasu basu samu warware ba, za ta ɗauki mataki na gaba.

Wasu daga cikin buƙatun ƙungiyar sun haɗa da;

  • Sabunta yarjejeniyar shekarar 2009
  • Bayar da kuɗaɗen gudanarwa ga jami’o’i
  • Biyan su haƙƙinsu na aikin da suka yi a baya na wata uku da rabi.
  • Tabbatar da an tura kuɗaɗensu da ake cirewa daga albashinsu zuwa ƙungiyoyinsu.

Shugaban ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya (ASUU) reshen Jami’ar Bayero ta Kano (BUK), Farfesa Ibrahim Tahir Suraj, ya shaidawa BBC cewa duk da cewa gwamnati ta fara biyan wasu buƙatunsu kamar tura kuɗaɗensu da ake cirewa daga albashinsu zuwa ƙungiyoyinsu, inda ya ce an biya su na wata ɗaya, babbar buƙatar da suke so gwamnati ta warwaremu shine na Sabunta yarjejeniyar shekarar 2009.

Karanta Wannan  Tambaya: Matar aure ce ta gayyaceni zuwa gidanta tace mijinta baya iya biya mata bukata amma yace yas yafe mata ta nemi wanda zai biya mata bukata shine na yi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *