
Kungiyar malaman Kwalejojin Ilimin Kimiyya da Fasaha ASUP ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin kwanaki 21 a biya musu bukatunsu ko su tafi yajin aiki.
Shugaban kungiyar, Comrade Shammah Kpanja ya bayyana hakan ga manema labarai a Abuja ranar Juma’a.
Yace daya daga cikin abubuwan da suke bukata shine a kafa hukuma me kula da ayyukan kwalejojin Ilimin kimiyya da fasaha.
Sannan kuma ya kara da cewa auna neman a daidaita sakamakon kammaga kwalejojin ilimin kimiyya na HND da Kwalin Digiri da ake bayarwa bayan kammala Jami’o’i.