Kwamishinan ‘Yan Sanda Ba Shi Da Hurumin Hana Gudanar Da Bukukuwan Sallah A Kano, Cewar Gwamnatin Kano
Daga Muhammad Kwairi Waziri
A wata sanarwa da kwamishinan shari’a na jihar Kano Alh Haruna Dedari ya fitar. Inda yake cewa Kwamishinan ‘yan sandan yana karbar umarni ne daga sama ba daga wajen gwamnatin jihar ba, sannan kuma ba tare da neman shawara da babban jami’in tsaro na jihar ba ko amincewar kwamitin tsaro na jihar kuma ya bayar da umarnin dakatar da bukukuwa sallah a jihar Kano ba tare da yawun Gomnatin jihar ba.
Tambaya ta anan shi wanene ke ingiza Kwamishinan ’yan sandan Jihar ya kwace ikon da Gwamna yake dashi a jihar sa ?