
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, Kwanannan za’a daina dauke wutar Lantarki kwatakwata a kasar.
Hakan ya fito ne daga bakin ministan wuta, Adebayo Adelabu a wata ganawa da manema labarai a Abuja.
Ya bayyana cewa, gwamnati na kokari kan hakan kuma tuni suka fara ganin sakamako me kyau.
‘Yan Najeriya sun dade suna kukan rashin tsayayyar wutar lantarki.