Monday, September 21
Shadow

Matatar Dangote za ta fara rarraba mai kai-tsaye bayan rage farashinsa

Matatar man fetur ta Dangote ta sanar cewa za ta fara rarraba man kai-tsaye zuwa tashoshi a duk faɗin Najeriya daga ranar Litinin, 15 ga Satumba.

Kazalika, kamfanin ya rage farashin man fetur ga masu gidajen mai zuwa N820 kan lita ɗaya, inda gidajen man jihohin Legas da sauran jihohin yammacin Najeriya za su sayar da shi kan N841.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kamfanin na fitar a shafinsa na X.

Sai kuma Abuja da Rivers da Delta da Edo da Kwara za su sayar kan N851. Ta ce daga baya shirin zai karaɗe sauran jihohin ƙasar.

Kamfanin ya ce an yi wannan tsarin ne domin rage farashin rarraba man da kuma sauƙaƙa farashin a tashoshi, da kuma rage matsin tattalin arziki.

Karanta Wannan  'Yan majalisa sun tambayi ministan kudi Wale Edun ya gaya musu yanda aka yi da kudin tallafin man fetur da aka cire, saidai yace ba zai fada ba a gaban 'yan jarida saidai a sirri

Haka nan, ana sa ran tsarin zai amfani ƙananan masana’antu sama da miliyan 42 ta hanyar rage farashin makamashi da inganta ribarsu, in ji matatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *