
Rahotanni sun bayyana cewa, Tsohon Gwamnan Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso zai koma jam’iyyar ADC nan da ranar Laraba.
Rahoton yace Kwankwaso zai koma jam’iyyar ADC ne a garinsa inda ake tsammanin zai yanki katin jam’iyyar acan.
Rahoton wanda ya fito daga the Whistler yace a kwanakinnan, Kwankwaso ya gana da wasu jiga-jigan jam’iyyar na ADC wanda hakan yasa ake kara kyautata zaton komawarsa jam’iyyar.