Thursday, July 16
Shadow

Ku yi hakuri da rashin wutar da kuke fama da ita, zamu gyara>>Ministan wutar Lantarki ya baiwa ‘yan Najeriya hakuri

Ministan wutar Lantarki, Adebayo Adelabu ya baiwa ‘yan Najeriya hakuri kan rashin wutar da ake fama da ita a ‘yan kwanakinnan.

Ya bayyana hakane a ganawar da yayi da manema labarai a Abuja ranar Talata inda yace musamman a wannan lokacin zafin da ake ciki rashin wuta akwai damuwa.

Yace amma suna bayar da tabbacin nan ba da jimawa ba zasu gyara wutar.

Karanta Wannan  Tela ya koka bayan da bankin Nirsal suka cire mai Naira dubu dari biyar(580,000) na bashin Kòbìd 19

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *