Kungiyar kwadago ta NLC ta soki Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu saboda abinda ta kira rashin tausai bayan kara farashin man fetur.
Wani jigo a NLC ne ya bayyanawa jaridar Punchng haka a yayin da kungiyar ‘yan kasuwar man fetur din ke cewa ba laifinsu bane maganar karin kudin man fetur din.
Hakanan kuma matatar man fetur ta Dangote ta bayyana cewa, karin farashin man fetur din ya samo asaline daga hauhawar farashin danyen man fetur wanda dashine ake yin man fetur din.
A ranar Juma’a data wuce, an sayar da man fetur din akan farashin Naira 1050 zuwa Naira 1150 akan kowace lita.
Mataimakin shugaba kungiyar kwadago ta NLC, Prof Theophilus Ndubuaku ya bayyana cewa, ya kamata shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a duk sanda irin bukatar abu haka ta taso ya rika saka masu ruwa da tsaki a lamarin dan tattaunawa.
Yace Najeriya ba ta mutum daya bace, ya baiwa shugaba Tinubu shawarar ya yi koyi da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo inda a duk sanda irin wannan lamari ya tashi, sai ya kira taron masu ruwa da tsaki dan tattaunawa.