
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar yaki da rashawa da cin hanci ta EFCC ta kwato kudade da yawa wanda bata taba kwato kamarsu ba tunda aka kafata.
Hukumar ce da kanta ta fitar da wannan sanarwa inda tace yawan kudaden data kwato sun kai Naira N364bn.
Sannan tace ta samu nasarar kulle mutane mahandama 4,11 jimullar kudaden da EFCC tace ta kwato sun hada da N364.6 billion, $214.5 million, £54,318.64, €31,265, CAD$2,990, sai kuma AUD$740.
Hukumar tace kuma wasu daga cikin kudaden an yi amfani dasu ne wajan ayyukan gwamnati dake amfanin ‘yan Najeriya kamar bayar da bashin karatu ga dalibai.