
Rahotanni sun nuna cewa, duk da cewa a yanzu akwai matatun man fetur dake tace mai a gida Najeriya, amma a shekarar 2024, yawan tataccen man fetur din da ake shigo dashi daga kasar waje ya nunka.
Rahoton hukumar kididdiga ta kasa, NBS ya bayyana cewa, kudin da ake kashewa dan shigo da man fetur din ya nunka inda yake a kaso 105.3 cikin 100 kamar yanda rahotanni suka nunar.
Inda a shekarar 2023 an kashe Naira N7.51tn wajan shigo da man fetur din amma a shekarar 2024 Naira N15.42tn ne aka kashe wajan shigo da tataccen man fetur din daga kasashen ketare.
Hakan na zuwane yayin da ake tsammanin cewa za’a samu raguwar dogaro da kasashen waje wajan siyen tataccen man fetur din musamman ma ganin matatar Dangote tana aiki hakanan an tayar da wasu matatun man fetur na Gwamnati.