
Rahotanni sunce sabon shugaban sojijin Ruwa da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nada watau Rear Admiral Idi Abbas, dan Asalin Jihar Filato ne domin a can aka haifeshi.
A lokacin da ya so shiga makarantar Horas da sojoji ta NDA dake Kaduna, ya je karamar hukumar sa inda ya nemi a bashi takardar shaidar zamansa dan karamar hukumar.
Amma sai aka ki bashi saboda Addininsa da kuma kabilarsa ta Hausa.
Sai ya tafi garin mahaifinsa, watau Kano kuma a can aka bashi takardar ya kai aka daukeshi aikin sojan.
Yau gashi ya zama shugaban sojojin Ruwa na Najeriya.
Zakaran da Allah ya nuna da chara….