
shugaban kungiyar Likitoci ta Najeriya, Professor Bala Audu ya bayyana cewa, Likitoci dubu 30 ne ake dasu a Najeriya.
Ya bayyana hakane a wajan wani taron kungiyar likitocin da ya wakana a Jihar Katsina.
Yace a shekaru 5 da suka gabata, Likitoci dubu 15 ne suka bar Najeriya zuwa kasashen Waje.
Yace kowane Likita daya yana ganin marasa Lafiya dubu 8. Wanda a ka’ida marasa lafiya dari shida ne ya kamata ace kowane likita na gani.