Macw tafi daukan ciki lokacin tana Ovulation, watau bayan ta gama haila a lokacin da take ganin wani farin ruwa me kamar kwai.
Wannan ruwa shine yake taimakawa maniyyin namiji ya shiga mahaifa ya zauna har ya hadu da kwan mace ya zama mutum.
Likitoci sun ce a wannan lokaci ne aka fi samun ciki, kuma suna bada shawarar ayi jima’i a wannan lokaci.
Saidai kuma sunce yawan yin jima’in baya kawo saurin daukar ciki.