
Rahotanni sun bayyana cewa, Ma’aikatan shari’a na Najeriya karkashin Kungiyarsu ta (JUSUN) sun nace akan tafiya yajin aiki gobe, Litinin, 2 ga watan Mayu.
Ma’aikatan bangaren babbar kotun tarayya ne zasu tafi yajin aikin inda bangaren kotun Koli suka fasa shiga yajinnaikin.
Wata majiya tace shugaban hukumar DSS ya zauna da ma’aikatan tsawon awanni 4 amma duk da haka sun ce ba zasu fasa tafiya wannan yajin aikin ba.
Sakataren kungiyar, Comrade Mohammed Isah yace zasu fara yajin aikin gobe Litinin inda yace yana kiran duka ma’aikatansu da su zauna a gida kada su je wajan aiki.
Saidai yace a goben ma akwai wani zama sa za’a sake yi.