Monday, December 16
Shadow

Ma’aikatar Gidaje da Ci Gaban Birane ta Tarayya, ta fara gina gidaje 500 a Jihar Kano

Ma’aikatar Gidaje da Ci Gaban Birane ta Tarayya, ta fara gina gidaje 500 a Jihar Kano.

Aikin ginin gidajen da aka yi wa laƙabi da “Renewed Hope Estate” na wakana ne a ƙauyen Lambu da ke ƙaramar hukumar Tofa.

Aikin ya haɗa da gina gida mai ɗaki biyu, ɗaki ɗaya, da kuma waɗanda ke da ɗaki uku.

A lokacin da ya kai ziyara wajen aikin, Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Ahmed Musa Dangiwa, ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda aikin ke tafiya. Ya ce aikin ba ya sauri kamar yadda aka tsara tun da fari.

Ya gargaɗi wanda aka bai wa kwantiragin da ya hanzarta ko kuma gwamnat ta ƙwace aikin daga hannusa. Ya kuma ce gwamnatin na son ganin an kammala aikin nan da ƙarshen shekara.”

Karanta Wannan  Babban Lauya, Femi Falana ya shigar da bukatar sakin yaran da aka kama da kuma basu ilimi kyauta, Sannan yace kotun ma bata da hurumin yi musu Shari'a

Kwantiragin, wanda manajan aikin Haruna Lawal ya wakilta, ya bai wa ministan tabbacin cewa za su ƙara ƙwazo don ganin sun kammala aikin kafin cikar wa’adin da aka ɗebar musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *