Rahotanni sun bayyana cewa mabarata dake yawo akan titi da jikin motoci dan samun abinda zasu ci sun kara yawa a babban birnin tarayya,Abuja.
Hakan na faruwane duk da yake Abuja na da motoci na Alfarma da kuma gidaje na alfarma da sauransu. Hakanan hukumomi na kokarin dakile lamarin ta hanyar tallafawa mabaratan.
Jaridar Daily Trust tace ta yi hira da wasu daga cikin mabaratan inda suka shaida mata cewa yawanci sun fito daga jihohin Arewa ne musamman wadanda ke fama da matsalolin tsaro.
Mabaratan dai sun fito ne daga jijohin Niger, Zamfara, Katsina, Nasarawa, Kano, Adamawa, Borno da sauransu.